Gwamna Ganduje Ya Biyawa Dalibai Kudin Jarrabawar NECO, NABTEB Da NBAIS

Alfijr ta rawaito Kwamishinan Ilimi na jihar Kano ya jinjinawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, bisa amincewa Da sakin kudin jarrabawa ga daliban dake shirin gama makarantar sikandire.

Majalisar zartarwa ta gwamnatin Kano ta amince da biyan sama da Naira Biliyan ɗaya, domin dai biyawa dalibai su rubuta Jarrabawar NECO, NBAIS da NABTEB a shekarar 2023.

Gwamnati ta amince da biya musu kudin ne, bayan da daliban sama da Dubu 66 suka samu nasarar cin kwasa kwasai 6 ciki har da turanci da lissafi.

Kwamishinan ya kuma umarci daliban da su je makarantun su, domin karbar takardar su tare da fara rijista.

Ya kuma shawarci daliban kan Kara jajircewa a jarrabawar da zasu zauna, domin fitar da Gwamnati kunya a wannan kokari da tayi wajen biya musu wannan kudi.

Wata sanarwar da aka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar Ilimi ta Kano Aliyu Yusuf, kwamishinan ya godewa dukkan masu ruwa da tsaki da suka jajirce wajen ganin an samu nasarar biyan kudin ga daliban yan asalin jihar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *