
Alfijr ta rawaito cikin daren ranar Asabar wasu fusatattun matasa sun yi dirar mikiya kan ƴan fashin wayar a unguwar Kabuga dake birnin Kano, har suka ƙone Baburin adaidaita sahun ɗaya daga cikin yan Fashin waya.

Wani ganau ya shaidawa Alfijr cewar, ƴan fashin wayar sun yi yunƙurin aikata fashin, inda matasan da za a yi wa fashin wayar suka nemi taimakon jama ar da ke kusa da wajen.
Sai dai waɗanda ake zargin da fashin wayar sun ranta a na kare dukansu , sun bar baburin adaidaita sahun da suke aikata laifin fashin wayoyin jama’a da shi.

Ganau din ya bayyana cewar jama’ar da ke wajen sun ƙone Baburin adaidaita sahun ƙurmus.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ
Kai Amma Masha Allah wllh naji dadin wannan labarin Allah yakara tonamusu asiri yabayya duk Wanda sukeda hannu acikin wannan lamari
Dama tsoron su da akeji yasa suke cin karensu ba babbaka, Alhamdulillah yanzu jamaa sun fara zasuyi wa kansu Magani…. Ya Allah ka karawa Bawa Al’umma karfin gwiwar kare kansu Amin