An gano gawar wani dattijo mai shekaru 80 da haihuwa, mai suna Malam Rabiu, wanda aka fi sani da Na Allah Siraka a wata rijiya da ke Sabon Sara, Gidan Aminu Ado da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya raba wa manema labarai a daren Lahadi a Kano.
Saminu ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi.
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:00 na safe daga wani Hassan Abdullahi, cewa wani mutum ya fada a rijiya.
“Nan da nan muka aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:07 na safe,” in ji shi.
Jami’an kashe gobara sun fito da gawar Rabiu daga cikin rijiyar a mace in da yake zaune shi kadai a gidan.
An mika mamacin ga Hakimin unguwar Sabon Sara, Muhammad Salisu-Iman. In ji P R O Saminu
Ya kara da cewa ana kan binciken musabbabin faruwar lamarin yanzu haka.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb