Daga Nazifi Kwankwaso
Ya bayyana cewa duba da irin haɗarin da gas ɗin ke ɗauke dashi, zai iya fashewa indan ba ayi auneba, hakan zata iya kaiwa da anyi asarai rayukan da dukiyoyin al’umma.
Alfijir Labarai ta rawaito shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau Laraba.
“Inda ya bayyana cewar Nau’in gas ɗin da direbobin Adaidaita sahun ke amfani da shi ba shi ne irin wadanda ake amfani da shi a ababen hawa ba”.
Yace saboda waɗan’nan dalilaine, yasa ya zama wajibi Hukumar ta kama duk wani direban Adaidaita sahun da aka samu yana amfani da gas ɗin maimakon Fetur.
A wani cigaban kuma, shugaban Hukumar KAROTA ya ce an haramtawa jami’an KAROTA yin amfani da Gora a kan titin Kano.

Yace daga cikin nau’in horon sanin makamar aiki da ake baiwa jami’an za su iya gudanar da aikin su ba tare da amfani da Gora ba.
A cewarsa yin amfani da Gora ya saɓa da dokar da ta kafa Hukumar ta shekarar 2012.
Ya kara da babu wata doka data bayyana inda jami’an KAROTA za su yi amfani da Gora, “don haka ba za mu sauka daga tsarin doka mu yi abinda ya saɓa da tsarin doka ba
Ya ƙara da cewa ƙwarewar jami’i da iya mu’amalarsu da jama’a ita ce za ta taimaka musa a bakin aikinsu a mai makon amfani da gora.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/BW0j8s7exuQ7ojpyCVMtfI