An kaddamar da bincike a kan zargin janye sojojin Daga Makarantar ‘Yan Mata ta Maga a Kebbi kafin yan bindiga su kai hari.

IMG 122403 241125 1763983468902

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta kaddamar da bincike a kan zargin janye sojojin da aka tura don su yi gadin Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a jihar Kebbi jim kadan kafin yan bindiga su kai hari.

Binciken ya taso ne sakamakon korafin da Gwamnan Jihar Kebbi, Dokta Nasir Idris, ya yi yana zargin cewa an janye dakarun tsaron ne mintuna 30 kacal kafin maharan su kai hari makarantar.
Gwamnan ya nemi rundunar sojin Nijeriya ta yi masa bayani mai gamsarwa kan dalilin daukar wannan mataki a daidai lokacin da ake bukatar tsaro a makarantar.

Da yake mayar da martani, Daraktan yada labara na hedikwatar tsaro ta kasa, Manjo-Janar Michael Onoja, ya tabbatar da cewa hedikwatar tsaro tana sane da zargin kuma tana bitar yadda aka tsara aikin sojojin a lokacin harin.
Ya ce  ko da yake ana tura sojoji ne bisa bayanan sirri na tsaro, rundunar a shirye take ta hukunta duk wanda aka samu da sakaci tare da gyara kurakuran da aka gano nan take.

Rundunar ta sha alwashin cewa ceto daliban jihar Kebbi da ma na jihar Neja da aka sace shine babban aikinta a yanzu.

Trust Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *