An kama Kanin Kwankwaso Da Wasu Kan Zargin Badakalar Samar Da Magunguna A Kananan hukumomin Kano

Screenshot 20240821 091228 WhatsAppBusiness

Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ta kama Garba Musa Kwankwaso, dan uwa ga dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Alfijir labarai ta ruwaito an kuma kama babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi, da kuma shugaban kungiyar kananan hukumomin jihar Kano (ALGON), bisa zargin badakalar samar da magunguna da ta shafi kananan hukumomi 44 na jihar.

An fara binciken ne tare da cafke Alhaji Mohammed Kabawa, babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, bisa zarginsa da hannu a badakalar samar da magunguna ta biliyoyin naira, bayan haka an kuma tsare wasu da ake zargi da hannu a cikin shirin.

Daga cikin wadanda aka kama akwai Abdullahi Bashir, shugaban kungiyar ALGON reshen jihar Kano kuma shugaban karamar hukumar Tarauni.

Ana zarginsu ne da hada baki wajen bayar da kwangilar samar da magunguna ga Novomed Pharmaceuticals a kananan hukumomi 38 na jihar Kano, bisa zargin saba dokar sayan magunguna.

A binciken farko da hukumar ta gudanar, kowacce daga cikin kananan hukumomi 38 ta biya Novomed naira miliyan 9.1 domin siyan magunguna.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa ba a ba su magungunan ba. Wani bincike ya nuna cewa an kama Musa Garba Kwankwaso, Manajan Daraktan Kamfanin Magunguna na Novomed kuma kane ga Sen. Rabiu Kwankwaso.

An ce dukkan wadanda ake zargin suna bayar da hadin kai ga tawagar binciken Hukumar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Kabiru I. Kabiru, ya tabbatar da kamen tare da bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.

Kabiru ya jadadda cewa hukumar na aiki tukuru domin bankado badakalar da aka yi da kuma gurfanar da waÉ—anda suka aikata laifin.

WaÉ—anda ake zargin dai na ci gaba da zama a hannun hukumar yayin da ake ci gaba da bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *