Wannan shi ne Brigadier general Nimrod Aloni, Janar din sojin isra’ila wanda mayakan gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas suka kama a harin ramuwar gayya da suka kaddamar a yau Asabar da nufin martani kan kisan kare-dangin da isra’ilan ke yi wa Palestine.
Alfijir Labarai ta rawaito cewa sama da sojin isra’ila 22 ne suka mutu a harin na yau Asabar yayin da wasu rahotanni ke cewa zuwa yanzu an an kashe sama da sojin isra’ila 50 tare da kama wasu masu yawa.
A halin yanzu dai isra’ila ta ce ta kaddamar da hare-hare a zirin Gaza yayin da al’ummar Falasdinawa suke ci gaba da kaddamar da hare-hare kan isra’ila ta sama, kasa da kuma ta ruwa.
Wani jami’in gwamnatin Isra’ila ya ce su a wajen su wannan harin na Falasdinawa kasar Iran ce ta kaddamar akan su domin ita ce ke ba su makamai da kudade, don haka za su rama akan ta.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo
Alhamdullilah
Masha allah allah yakarabawa
Palestine sa a