Gidan Talabijin na Qausain TV ya nada fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango a matsayin Darakta Janar na gidan Talabijin.
Alfijir labarai ta rawaito shugaban kamfanin Qausain, Alh Nasir Idris ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa nadin Adam Zango a matsayin Darakta Janar din ya fara aiki nan take.
A cewar sanarwar, an amince da nadin ne yayin wani taron hukumar daraktocin kamfanin.
Alhaji Idris ya kara da cewa an nada tsohon Gwamnan Soja na Jihar Kano, Kanar Sani Bello (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar daraktocin kamfaninm
“Nadin Bello a matsayin Shugaban hukumar daraktocin kamfanin na tsawon shekaru hudu ne, kamar yadda dokar Kamfanoni ta tanada.
Idris ya ce an nada tsohon ministan sadarwa Farfesa Isa Pantami a matsayin mai sanya idanu kan harkokin shugabannin kamfanin.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj