Kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karɓe filin.
Alfijir Labarai ta rawaito kamfanin BUA ya fitar da dogon jawabi a ranar Juma’ar nan, a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dangote Group ya jefe shi da shi.
Kamfanin na BUA ya ɗauko tarihi tun daga 1991 lokacin da aka yi wahalar sukari, amma sai aka yi sa’a Abdul Samad Rabi’u ya na da sukari a ƙasa, sai Aliko Dangote ya nemi a saida masa sukarin, sai a karshe lamarin ya ƙare a kotu, kamfanin ya ce haka Rabi’u ya jajirce na watanni uku.
Har ila yau, kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karɓe filin, wanda a dalilin wannan abin da ya faru a gwamnatin Olusegun Obasanjo, BUA ya yi asarar filin da ya karɓi aro daga hannun kawun na Dangote, sai bayan shekara Rabi’u ya iya komawa harkar sukari, yanzu kamfaninsa ya zarce kowa a yammacin Afrika, a cewar wasikar.
Wasikar ta ce haka kamfanin ya yi ta fama bayan samun lasisin kafa kamfanin siminti, BUA ya ce sam ƙalubalen nan ba su iya taka masu burki ba.
Amma a wani rahoto da Daily Nigerian ta fitar, an ji kamfanin Dangote ya ƙaryata zargin badaƙalar kuɗin waje, ya ja kunnen masu yin sharri.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp