An Sanya Dokar Hana Fita A Jihar Kaduna A Yau Litinin

Alfijr ta rawaito an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Sabon Garin Nasarawa-Tirkaniya a karamar Hukumar Chikun.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da sanya dokar ta-baci ta sa’o’i 24 nan take a yankin Sabon Garin Nassarawa-Tirkaniya da ke karamar Hukumar Chikun.

An cimma wannan matsaya ne biyo bayan tabarbarewar doka da oda da ta kai ga kashe wasu ‘yan kasar guda biyu a wani rikici da ya barke a birane.

An umurci hukumomin tsaro da su aiwatar da dokar hana fita a wurin da aka ce, domin dawo da zaman lafiya yayin da ake ci gaba da bincike.

Don haka an yi kira ga ‘yan jihar da su kiyaye dokar hana fita a wannan wuri, wanda zai fara aiki nan take.

Kamar yadda Samuel Aruwan Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ya sanyawa hannu a yau Litinin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *