Alfijr ta rawaito kungiyar ‘yan jaridun ta yanar gizo sun ta taya zababben gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) murnar lashe zaɓen gwamnan Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban riko na kungiyar na jahar kano Yakubu Salisu wada da ya rabawa manema labarai
Yace Nasarar Abba ba ta bada mamaki ba, saboda dimbin farin jini, iya aiki da tarihinsa na tsawon shekaru wanda hakan ya ba shi matsayi na musamman a zukatan al’ummar jihar kano.
Sanarwar ta kara da cewa, kanawa sun kyautata zaton cewa zai mayar da jihar Kano cikin bunkasar tattalin arziki, wadatar masana’antu da kasuwanci gami da samar da ababen more rayuwa da ci gaban bil’adama.
A matsayinmu na kwararriyar kungiya wacce ta taka rawar gani wajen yada manufofin jam’iyyar NNPP da na zababben gwamnan Kano ga al’ummar Kano, muna alfahari da kasancewa tare da mai girma Abba Kabir Yusuf, kuma mun yi imanin zai samar da ribar dimokuradiyya ga mutanen kirki na jihar.
Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su hada kai tare da ba shi duk wani goyon bayan da ake bukata domin ciyar da jihar gaba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇