Alfijr ta rawaito majalisar zartarwa ta jihar Katsina, wadda Gwamna Aminu Bello Masari ke Jagoranta ta amince da shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina ya gaggauta ajiye mukaminsa,
Sauke shi daga muĘamin ya biyo bayan rahotan da Gwamna ya kafa da ya ba shi shawara, kan rahotan da aka gabatar Masa akan Korafe-korafe da Aka gabatar a kansa
Majalisar ta kuma umurci shima shugaban hukumar gudanarwar na jami’ar ya Umaru Musa Yar’adua Farfesa Mu’uta Ibrahim da ya gaggauta yin murabus daga bisa mukamin nasa nan take
Mai baiwa Gwamna shawara kan Ilimi mai zurfi, Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya, ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema Labarai, Jim kaÉan da fitowa daga zaman majalisar zartarwa a gidan gwamnatin jihar Katsina jiya Laraba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai š