Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya ce nan ba da jimawa ba majalisar dattawa za ta sake nazari kan dakatarwar da aka yiwa Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku kan zargin cewa an yi kasafin naira tiriliyan 28.78 na shekarar 2024 dayakai naira tiriliyan 3.7.
Alfijir labarai ta rawaito Akpabio ya bayyana haka ne bayan dawowar sa Najeriya bayan wata ziyarar kwanaki bakwai da ya yi a birnin Geneva na kasar Switzerland don halartar taron kungiyar IPU karo na 148.
Ko da yake ya ce har yanzu bai ga wata takarda daga Sanata Ningi ba, ya bayyana fata cewar nan ba da dadewa ba dan majalisar Bauchi zai koma bakin aiki majalisa.
Sanatan Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi da aka dakatar, an ce ya rubutawa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da shugabancin majalisar ta hannun lauyansa, Femi Falana, SAN, inda ya bukaci a dage dakatarwar da aka yi masa.
Falana ya jaddada cewa idan har ba a dage dakatarwar da aka yi masa ba nan da kwanaki bakwai masu zuwa, zai kai majalisar dattawa gaban babbar kotun tarayya.
Falana ya kuma kara da cewa, baya ga tauye hakkin Ningi, majalisar ta kuma take hakkin al’ummar mazabar Bauchi ta tsakiya na samun wakilci a majalisar na tsawon watanni uku. Ya kuma bayyana cewa dakatarwar ya sabawa sashe na 111 na kundin tsarin mulkin kasa da kuma sashe na 13 na dokar kare hakkin dan Adam na Afrika.
Majalisar Dattawa, a ranar 12 ga Maris, 2024, ta dakatar da Sanata Ningi na tsawon watanni uku, saboda wata hira da ya yi da Sashen Hausa na BBC, inda ya yi zargin cewa Naira Tiriliyan 3 a cikin kasafin kudin 2024 ba a iya gano dalilan saka ta cikin kasafin kudin ba.
Haka kuma dakatarwar ta kai ga murabus din dan majalisar dan asalin jihar Bauchi daga mukaminsa na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa inda nan take jam’iyyar APC ta maye gurbin Sanata Abdulaziz Yar’adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk