Daga Aminu Bala Madobi
Ambaliyar ruwan sama ya janyo katsewar wani muhimmin bangare na babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri a garin Malori-Guskuri dake karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi.
Alfijir labarai ta ruwaito bayanai sun tabbatar da cewa ci gaban da aka samu ya sa hanyar ba a iya wucewa, lamarin da ya tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da bin wasu hanyoyi.
Da yake jawabi a wurin, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jaddada mahimmancin hanyar, wadda ke zama muhimmiyar hanyar da ta hada yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Najeriya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shiga tsakani tare da gyara bangaren babbar hanyar da ta lalace domin saukaka zirga-zirgar kayayyaki da ayyukan yau da kullum, domin amfanin ‘yan kasa baki daya.
‘’Hakan wani sako ne na gaggawa da ya aikewa gwamnatin tarayya, domin hana afkuwar mace mace da wahalhalun da ke tattare da babbar hanyar.
Gwamna Mohammad ya kara da cewa gwamnatin sa za ta samar da hanyoyin da suka dace, don kula da wasu hanyoyin gwamnatin tarayya a jihar yayin da ake tsaka da damina.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj