Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.
Alfijir labarai ta rawaito Ƴan majalisar sun tsige Shaibu, wanda ke fafatawa da Gwamna Godwin Obaseki a safiyar yau Litinin.
Daga cikin mambobi 20 da suka halarci zaman majalisar, 18 sun kada kuri’ar amincewa da rahoton kwamitin yayin da daya ya ki amincewa.
Shaibu ya ki amsa gayyatar da kwamitin mutum bakwai ya yi masa wanda ya binciki zargin da ake masa.
Bayan ya ki amincewa, kwamitin karkashin jagorancin mai shari’a S.A. Omonua (rtd) ya rubuta rahotonsa tare da ba da shawarar tsige shi, yana mai cewa Shaibu ya ki amfani da damar kare kan sa.
Sai dai kuma wani rahoto da Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa gamna Godwin Obaseki ya nada Omobayo Marvelous Godwins, Injiniya mai shekaru 38 a matsayin mataimakinsa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk