Ana Wata! Dillalan mai sun yi barazanar rufe gidajen mai dubu 30 a Nijeriya

Fetur

Dillalan mai a karkashin kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya, IPMAN a jiya Talata, sun bayyana cewa za su rufe gidajen mai guda dubu 30 da ‘yan kungiyar IPMAN ke gudanarwa a fadin kasar nan idan har gwamnatin tarayya ta gaza biyan su bashin Naira biliyan 200 da su ke bin gwamnati.

Alfijir Labarai ta rawaito IPMAN ta ce musamman hukumar kula da harkokin man fetur na ruwa da tsandauri ta Najeriya, NMDPRA ta ki yafe basussukan da ke ci gaba da karuwa tun watan Satumban 2022.

Ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta IPMAN reshem tashoshin dakin mai, Yahaya Alhassan ya fitar a Abuja, kan rashin biyan kudaden da ‘yan kasuwa ke bi ya ce IPMAN tana kula da gidajen mai sama da dubu 30,000 a Najeriya.

Su waɗannan kudade diyya ne da gwamnati ke yi biya wa ‘yan kasuwar man don jigilar man fetur da aka yi lodi daga gidajen man fetur zuwa jihohi daban-daban a fadin kasar nan.

Alhassan ya ce sakamakon gazawar da hukumar ta NMDPRA ta yi na biyan Naira biliyan 200 “zai yi muni matuka, domin duk wani gidan mai da ke fadin Najeriya, daga Arewa zuwa Kudu, daga Gabas zuwa Yamma za a rufe.

Ya kara da cewa, “A matsayinmu na kungiyar IPMAN, mun dauki kowane mataki a baya don ganin mun ceto wannan al’amari mai cike da ban tausayi, wanda kuma mun san ba zai yi wa ‘yan Nijeriya dadi ba, amma a halin yanzu ba mu da wani zabi da ya wuce mu fita gaba daya a cikin ‘yan kwanaki kadan masu zuwa, don magance wannan mummunar dabi’a ta hanyarmu, wanda zai haifar da wahala da haɗari ga ‘yan Najeriya,” in ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *