Daga Aminu Bala Madobi
Majalisar Wakilai a Najeriya ta bukaci Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta kasa NERC da ta dakatar da shirin aiwatar da sabon harajin biyan wutar lantarki ta kasa.
Alfijir Labarai ta rawaito Kiran ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa Nkemkanma Kama na jamiyyar Labor Party daga jihar Ebonyi (LP-Ebonyi) a kudirin da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.
Idan za a iya tunawa, hukumar kukada wutar lantarki ta kasa a ranar 3 ga Afrilu, ta amince da karin kudin harajin wutar lantarki ga kwastomomin da ke cin awoyi 20 na wutar lantarki a kullum wanda aka kebe a matsayin masu amfani da B and A.
Ya ce hujjojin da aka gabatar sun nuna amincewar da NERC ta bayar ya haifar da tashin gwauron zabi na kashi 300 ga wasu masu amfani da su.
“Wannan kudiri ya yi kira ga ‘yan majalisa su shiga tsakani, tare da jaddada wajibcin tsarin mulki da na mu na da’a na magance rikicin da kuma rage nauyi a kan ‘yan Najeriya.
A hukuncin da ya yanke, kakakin majalisar, Tajudeen Abbas ya ce ya kamata kwamitocin da abin ya shafa su tabbatar da bin ka’ida.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk