Ana Wata: Jam’iyyar NNPP Ta Kori Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Kwamatin ya yi gargadin cewa, rashin bayyana gaban kwamitin ladabtarwar, zai iya jawi korar Kwankwaso daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada a 2022 (kamar yadda aka gyara).

Alfijir Labarai ta rawaito kwamitin zartarwa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ya kori Sen. Rabi’u Kwankwaso, sakamakon kin bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Idan zaku tuna cewa tun da farko shugabannin jam’iyyar sun dakatar da Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023 a babban taron kasa da aka yi a ranar 29 ga watan Agusta a Legas.

Majalisar zartaswa ta kasa, NEC, ta NNPP ta kafa kwamitin ladabtarwa tare da umarce ta da ta gayyaci Kwankwaso domin ya kare zarge-zargen cin hanci da rashawa na jam’iyya da karkatar da kudaden jam’iyya/kamfen cikin kwanaki biyar.

Kwamatin ya yi gargadin cewa, rashin bayyana gaban kwamitin ladabtarwar, zai iya jawi korar Kwankwaso daga jam’iyyar kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada a 2022 (kamar yadda aka gyara).

Sakamakon haka, Abdulsalam Abdulrasaq, Mukaddashin Sakataren Yada Labarai na NNPP, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Legas, ya ce hukumar zaben ta kori Rabiu Kwankwaso ba tare da bata lokaci ba, saboda ya ki amincewa da gayyatar kwamitin.

Abdulrasaq ya ce: “kwamatin jam’iyyar ta kasa ta yi zaman gaggawa a ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba, inda ta yanke hukunci kamar haka:

“Bayan kin bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gaban kwamitin ladabtarwa da ya zauna a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta bayan ya yi na’am da shi.

An gayyace shi a rubuce, an kore shi daga Jam’iyyar NNPP nan take.

“Za a kai rahoton tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa wuraren da suka dace domin amsa tambayoyi kan kudi da suka shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma.”

NAN ta ruwaito cewa rikicin cikin jam’iyyar NNPP ya faro ne lokacin da NWC na jam’iyyar da ke biyayya ga Kwankwaso, ta sanar da dakatar da wanda ya kafa NNPP, Dokta Boniface Aniebonam da sakataren yada labarai na kasa, Dr Agbo Major a ranar 24 ga watan Agusta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Slide Up
x

One Reply to “Ana Wata: Jam’iyyar NNPP Ta Kori Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *