Ana Wata! kamfanonin rarraba wutar lantarki ya kara farashin wutar a Nijeriya

FB IMG 1712156301117

Daga N68, ƴan Nijeriya za su koma biyan N200 kuɗin wutar lantarki a duk awa ɗaya — Rahoto

Kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya ruwaito daga ranar Talata cewa, za a bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki su kara farashin wutar lantarki zuwa N200 a kowace kilowatt daga Naira 68 duk sa’a ɗaya ga masu shan wutar lantarki mazauna birane daga wannan watan.

Alfijir labarai ta rawaito cewa a rahoton na Bloomberg, wadannan kwastomomi na wakiltar kashi 15% na al’ummar kasar da gwamnati ta ce suna amfani da kashi 40% na wutar lantarkin kasar, in ji hukumar.

Bloomberg ya ce Najeriya na shirin kusan rubanya farashin makamashi a cikin makonni masu zuwa.

An ruwaito wasu mutanen da ke fadar shugaban kasa da ke da masaniya kan lamarin suna cewa hakan na da nufin jawo hankulan sabbin masu zuba jari da kuma kawo karshen kashe kusan dala biliyan 2.3 da gwamnati ke yi 2qjen biyan tallafi wutar lantarki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan fallasa na zuwa ne biyo bayan sanarwar da hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa, NMDPRA, ta fitar a ranar Litinin da ta gabata na karin farashin iskar gas da ake amfani da shi wajen samar da sama da kashi 70% na wutar lantarki a Najeriya.

Da Daily Trust ta tuntubi Babban Manajan Hukumar Wutar Lantarki ta Ƙasa, NERC, Dakta Usman Arabi a jiya, bai amsa kiran waya da sakonnin kar-ta-kwana da aka aika a wayarsa ba.

Amma Bloomberg ya ruwaito Bayo Onanuga, mai magana da yawun fadar shugaban kasar yana cewa, “NERC za ta yi wani jawabi dangane da tattaunawar da ta yi da kamfanonin rarrabawa da samar da kayayyaki nan gaba kadan,”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *