Labari Mai Dadi Wasu Matasa Sun Ragargaza Masu Garkuwa Da Mutane A Kano

IMG 20230923 WA0013

Rundunar hadin gwiwa dake aikin samar da tsaro a karamar hukumar Gwarzo, Kano, ta dakatar da wani yunkuri da matasan unguwar Ruga dake karamar hukumar suka yi na kashe wasu mutane biyu da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban riko na karamar hukumar Gwarzo da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa da jami’an tsaron yankin, Dokta Mani Tsoho wanda a bayyane ya kadu matuka game da yadda matasan suka fusata har suka lalata motocin jami’an tsaro, ya bukaci Matasa da al’ummar yankin da su kwantar da hankula tare da bayar da umarnin a kamo masu laifin cikin gaggawa.

Mani ya yi kira ga al’ummar yankin da su kasance masu bin doka da oda a nan gaba.

“Abin da ya dace a yi shi ne mika wadanda ake zargi da aikata laifuka ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Mani Tsoho.

A zantawarsa da manema labarai wani mazaunin garin Riga, mai suna Shugaba Sani Mato, yace wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutanen sun fito ne daga jihar Katsina kuma sun dade suna tayar da hankulanmu shi yasa yau muka far musu.

Sani Mato ya ce garin na Riga dake mazabar Kutama yayi iyaka ne da jihar Katsina.

A Sanarwar da jami’in yada labarai na shiyyar Gwarzo Rabi’u Khalil ya aikowa kadaura24 yace, a nasa jawabin Hakimin Gwarzo Barde Kerarriyya Alh.Shehu Kabiru Bayero ya yabawa kokarin jami’an tsaro na dawo da zaman lafiya a cikin al’ummar da abin ya shafa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *