Ana Wata! Ogan Boye Ya Ajiye Mukaminsa Na Mai Baiwa Gwamna Shawara

FB IMG 1724163862583

Amb. Imam Yusuf wanda aka fi sani da Oga Boye ya Ajiye mukaminsa na mai baiwa gwamnan jihar kano shawara kan harkokin matasa.

Alfijir labarai ta ruwaito Ogan Boye ya Mika takardar ajiye aikin nasa ne a Ofishin Sakataren gwamnatin jihar kano a wannan rana ta talata.

Imam Yusuf ya ajiye mukaminsa nasa ne domin ya tsayawa takarar shugabancin Karamar Hukumar Nassarawa a cikin jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya.

Idan za’a iya tunawa dokar Zaɓe ce ta ce dole duk mai sha’awar tsayawa takarar wata kujerar sai ya ajiye duk wani Mukami da aka nada shi kwana 90 kafin zaben.

Hakan nuni da cewa Ogan Boye ya shiga cikin jerin wadanda suke takarar shugabancin Karamar hukumar Nasarawa a zaɓen da za’a gudanar a ranar 30 ga watan Nuwanba mai zuwa.

Kadaura24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *