Daga Rabiu Usman
Alfijr ta rawaito anyi kira ga kabilar Kanuri mazauna jihar kano dasu fito suyi zaben shekarar 2023 babu tashin hankali ko hayaniya yayin gudanar da zaben.
Mai Girma wakilin shehun Borno a jihar kano kuma Sarkin Kabilar Kanuri mazauna kano Alhaji Mustapha Lawan (Mai Kanuri) ne yayi kiran yayin ganawar sa da wakilin mu a yammacin Litinin.
Yana mai cewar, Sarkin ya Umarci dukkannin kabilar Kanuri mazauna kano dasu fito kwansu da kwarkwata su zabi wanda suka ga ya Chanchanta a wajen su ba tare da tashin hankali ko hayaniya ba yayin gudanar da zabukan da muke tunkara na 2023.
Daga nan yayi Addu’ar samun zaman lafiya ga jihar kano da Borno dama kasa baki daya.
A karshe yace ya zama wajibi ga duk Dan Kasa na gari ya fito yayi zabe sannan ya baiwa Jami’an tsaro Hadin kai wajen yin aikin su kamar yanda doka ta tanada.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux
Mashaa Allahu noted sir