ASUU ta fara haɗa kan mambobinta domin fara yajin aiki a Nijeriya

FB IMG 1759757474382

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta fara hada kan mambobinta a dukkan jami’o’in kasar domin fara yajin aikin kasa baki daya da ta tsara.

Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan shiru da gwamnatin tarayya ta yi duk da sanarwar da aka aika wa hukumomin da suka dace, ciki har da ministocin kwadago da ilimi.

Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, a wata wasika da aka fitar ranar 5 ga Oktoba, 2025, ya bayyan cewa babu wani ci gaba da aka samu wajen magance matsalolin da suka dade suna janyo sabani tsakanin gwamnati da kungiyar.

Ya ce majalisar zartarwa ta ASUU ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 14 don kammala yarjejeniyar da aka tsara tun watan Fabrairu, 2025, sannan za ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu idan ba a dauki mataki ba.

ASUU ta ce manufar yajin aikin ita ce tilasta gwamnati ta sanya hannu da aiwatar da sabuwar yarjejeniya, da kuma sake farfado da tsarin jami’o’in kasar domin gogayya da sauran kasashe.

Daily Trust

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *