Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka kan shirin da gwamnatin tarayya ta yi na kara kudin harajin harajin VAT.
Alfijir Labarai ta rawaito Atiku ya bayyana hakane cikin wani shirin siyasa a gidan talabijin na Channels Politics Today,
Taiwo Oyedele, Shugaban kwamitin shugaban kasa kan kasafin kudi da gyaran haraji, ya ce kwamitin na gabatar da wata doka ga Majalisar Dokoki ta kasa don kara haraji daga kashi 7.5% zuwa 10%.
Ya ce,dokar da zamu gabatar wa majalisar dokokin kasar mai da harajin VAT kashi 7.5% ya koma kashi 10 cikin 100 daga shekarar 2025. Ba mu san ko yaushe za su iya zartar da dokar ba.
Amma da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar Lahadi, Atiku ya ce matakin dai ya biyo bayan karin farashin man fetur da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya yi ya kara matsalar tsadar rayuwa a cikin al’umma da kuma kara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin kasar.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj