Ba muyi komai a ƙudundune ko a rufa-rufa ba – In Ji tsohon Shugaban kasa Buhari

IMG 20240118 080409

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ba su tafiyar da gwamnatin sa cikin rufa-rufa ko wata ƙumbiya-ƙumbiyar da aka riƙa ɓoye ayyukan gwamnati a cikin sirri ba.

Alfijir labarai ta rawaito Buhari ya shaida haka lokacin da yake jawabi wurin taron ƙaddamar da littafi, wanda tsohon Kakakin Yaɗa Labaran sa, Femi Adesina ya rubuta.

Adesina ya rubuta littafin mai ɗauke da bayanan yadda ya yi aiki tare da Buhari tsawon shekaru takwas a Fadar Shugaban Ƙasa, Aso Villa, Abuja. An ƙaddamar da littafin a ranar Talata.

Buhari wanda ya halarci taron, wannan ne zuwan sa Abuja na farko, tun bayan saukar sa daga mulki, a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Ya ce ya ji farin ciki ganin ga shi Abuja, watanni takwas a karon farko bayan saukar sa daga mulki.

Daga nan ya gode wa Shugaba Tinubu da ya samu dama da lokacin halartar taron ƙaddamar da littafin.

Buhari ya ce alaƙar sa da Tinubu a ko yaushe garau take.

Daga nan ya gode wa waɗanda suka yi tafiyayya har Daura suka kai masa ziyara.

Ya ce ba wani abu ya kawo shi Abuja ba, sai litattafai biyu da aka wallafa kuma duk a kan sa.

Ɗaya wanda Femi Adesina ya rubuta, ɗaya kuma wanda kundin litattafai ne guda biyu, wanda Dakta Udu Yakubu ya gyara bayan an taskace.

Ya ce shi dama ɗan Adam ya na da saurin mantuwa. Amma litattafan da aka rubuta za su kasance matashiya kan shekaru takwas ɗin gwamnatin sa a nan gaba.

“Amma babban abin dogaron mu shi ne ba mu yi komai ƙudundune cikin rufa-rufa ko wata ƙumbiya-ƙumbiya. Saboda mun san akwai ranar da za a fito da kowane rekod na abin da muka aikata.

“A yayin da muke gudanar da mulkin mu, akwai abubuwa masu tsauri da muka zartas, waɗanda jama’a suka ɗanɗana kuɗar abin. To muna dai ƙara fahimtar da su cewa ba da mugun nufi ko ƙeta muka zartas da su ba. Dalili kenan a ƙarshen mulki na na bada haƙuri, na nemi afuwa.” Cewar Buhari

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *