Ba Za Mu Iya Ci Gaba Da Biyan Tallafin Wutar Lantarki Ba – Gwamnatin Tarayya

FB IMG 1707948578577

Gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cewa ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba saboda dimbin basussuka da ta ciyo.

Alfijir labarai ta rawaito ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a yau Laraba.

Adelabu ya ce dole ne kasar nan ta fara tafiya kan tsarin rashin dogaro da kai, domin a halin yanzu kasar na bin bashin Naira Tiriliyan 1.3 wanda ake sakawa a lantarki.

Ya ci gaba da cewa, Naira biliyan 450 ne kawai aka ware domin bayar da tallafi a bana, duk da cewa ma’aikatar na bukatar tallafin sama da Naira tiriliyan 2, ya kara da cewa a yanzu gwamnatocin jihohi za su iya samar da wutar lantarki ba tare da dogaro da tarayya ba domin samar da wutar lantarki ga jihohinsu.

Ya bayyana cewa, tashar ta ruguje har sau shida a tsakanin watan Disambar 2023 zuwa yanzu sakamakon karancin iskar gas.

Ministan ya kuma bayyana cewa an ware sama da Naira biliyan 50 a cikin kasafin kudin shekarar 2024 don kafa kananan hanyoyin sadarwa don samar da wutar lantarki ga wurare daban-daban.

Ya kuma gargadi ‘yan kasuwar rarraba wutar lantarki (DisCos) su tashi tsaye kan lamarin duk kuma wanda aka samu da karya doka to a kwace lasisin su.

Ministan ya kuma bayyana cewa ya tuntubi Nuhu Ribadu, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) domin ya taimaka wajen kare hanyoyin wutar lantarki.

Kalaman ministan wutar lantarkin ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta mayar da tallafin man fetur da ya cire a lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *