Ba Zamu Lamunci Duk Wani Ƙoƙarin Tada Zaune-Tsaye Ba — In Ji ECOWAS

IMG 20251207 WA0174

Daga Aminu Bala Madobi

Ƙungiyar ECOWAS ta bayyana cewa ba za ta yarda da duk wani yunƙurin tayar da tarzoma ko tada hankalin jama’a a cikin kowace ƙasa mamba ba.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan bayyanar rahoton cewa an ayyana juyin mulki a ɗaya daga cikin ƙasashen yammacin Afirka.

A bayanin da kungiyar ta fitar, ta jaddada cewa tsaro, zaman lafiya da tsarin dimokuradiyya su ne ginshiƙai da ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare su ba. Ta ce za ta ci gaba da bibiyar al’amura domin tabbatar da cewa ba a kassara tsarin mulkin ƙasa ba.

ECOWAS ta kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda, tana mai cewa duk wani mataki da zai tada jijiyar wuya za a magance shi cikin gaggawa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *