Babbar Magana! Wata Kura Ta Tsere Daga Kejinta A Jos

FB IMG 1720525014532

Al’ummar unguwar da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato, suna cikin fargaba bayan da Kura ta tsere daga kejinta a gidan ajiyar namun daji da ke yankin.

Alfijir labarai ta ruwaito lamarin dai ya faru ne tun a ranar Lahadi, wanda ana sa ran dabbar ba ta yi nisa da harabar gidan ajiyar namun dajin ba saboda girma da wajen ke da shi.

Babban Manajan hukumar yawon bude ido ta Jihar Filato, Chuwang Pwajok, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da shaida wa mazauna yankin cewa su kwantar da hankalinsu domin ana kokarin gano inda dabbar ta shiga don dawo da ita kejinta.

Kazalika ya ƙaryata raɗe-raɗin da ke yawo na cewa yunwa ce ke sanadin tserewar dabbobin wanda ya ce wasu kejin ne sun tsufa amma gwamnati ta ɗauki matakan zamanantar da su nan ba da jimawa ba.

Idan ba a manta ba a shekarar 2015 wani zaki ya taɓa tserewa daga kejinsa a cikin babban gidan namun dajin na Jos.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *