Labari Mai Dadi! Tinubu Yayi Umarnin A Shigo Da Wasu Nau’in Kayan Abinci Domin Rage Radadin Da Ake Ciki

FB IMG 1718043976588

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarni ga ‘yan kasuwa su shigo da kayan abinci ba tare da sun biya kuɗin haraji ba tsawon wani lokaci.

Alfijir labarai ta ruwaito kayan abincin da Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin ta cire wa harajin har na tsawon kwanaki 150, sun haɗa da shinkafa, wake da irin su alkama da masara da sauran su.

Shugaban ya yi hakan ne domin a rage raɗaɗin tsadar kayan abinci da kayan masarufi, waɗanda suka addabi ‘yan Najeriya, babba da yaro.

Ministan Harkokin Noma, Abba Kyari, ya ce “Shugaba Tinubu ya amince da janye biyan haraji kan kayan abincin da za a shigo da su, har tsawon kwanaki 150 ba tare da an biya haraji ba,” “a kan kayan abinci irin su masara, alkama da sauran su.”

Tun daga ranar da Tinubu ya cire tallafin fetur ‘yan Najeriya suka afka cikin raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar kayan abinci da masarufi.

Wannan lamari ya ƙara tsawwala farashin kayan abincin da ake shigowa da su da kuma nan cikin gida.

Sanarwar ta ƙara da cewa ita ma Gwamnatin Tarayya “za ta shigo da metrik tan 250,000 na alkama da metrik tan 2500,000 na masara. Alkamar da nasarar duk samfarera ne za a shigo da su, sai a bayar ga masu ƙanana da matsakaitan masana’antun casa domin su sheƙe su tare da cashewa.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *