Babu gurin da nake samun nutsuwa kamar gurin Mauludin Manzo S.A.W – Sarkin Bichi

IMG 20231023 WA0000

Mai Marataba Sarkin Bichi, Alh. Nasiru Ado Bayaro, ya ce babu wajen da yake jin dadin kasancewar sa face wajen Mauludin Annabi S.A.W.

Alh. Nasiru Ado Bayero, ya bayyana hakane a daren Asabar a wajen taron Mauludin da Mahmud Sa’eed Adahama, ya shirya a Unguwar G.R.A da ke Kano.

Mai Martaban ya ce, ” ba karamin farin ciki yake ji ba, idan akace ya halarci taron mauludi “.

Daga cikin wadanda suka halarci Mauludin, akwai Shugaban majalissar Shura ta jihar Kano, Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, inda ya ce rashin shugabanci na gari da bin doka da Oda da kyakkyawar mu’amula, wasu muhimman abubuwa ne da sai an gyara su za’a samu Al’umma ta gari.

Taron Maulidin da aka gudanar cikin Sa’o’i dai, ya maida hankali ne kan kara bayyanawa Al’umma daraja da girman da Manzo S.A.W ke da shi a wajen Allah madaukakin Sarki, kamar yadda masu jawabi su kayi.

Da yake zantawa da manema Labarai, game da makasudin shirya Mauludin, Mahmud Sa’eed Adama, wanda shi ke shirya taron Mauludin kowacce shekara, ya ce sukan shiryawa ne domin zaburar da Al’umma muhimmancin hidimtawa Annabi S.A.W.

A hannu guda shi ma da yake tsokaci kan yadda Matasa za su kasance masu son Manzon ALLAH, Khalifa Sheikh Hassan Gawuwana, ya bukaci Al’umma da su kasance masu koyi da dabi’un Ma’aiki S.A.W.

Masu kasidu daban-daban irin na yabon Ma’aiki ne dai suka rika rerawa cikin wake, yayinda wasu kuma suka rinka yi a cikin magana.

Manyan Malamai irin su Dr. Na Sidi Abubakar G/Dutse, da Malam Umar Sani Fagge, da sauran Malamai ne suka halarci taron.

IMG 20231023 WA0001
📸 Sarkin Bichi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *