Alfijr ta rawaito Hukumar ‘yan sanda ta kama wani yaro dan shekara ashirin mai suna Ghadaffi Sagir da ya kashe mahaifiyarsa da wani abu mai kaifi sannan ya shake ‘yarta a Kano.
Wanda ake zargin ya aikata laifin ne a daren Asabar da misalin karfe 11:00 na dare, a Rijiyar Zaki daura da Layin Dorawan yan Kifi, karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.
Da yake tabbatar da kamun ga Solacebase a ranar Lahadi, shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat, ya ce wanda ake tuhumar ya yi ikirarin cewa ya kashe matar mahaifinsa mai suna Malama Rabi ne saboda ita ce sanadin rabuwa tsakanin mahaifiyarsa da mahaifinsa, Malam Sagir Maimagani.
Ya ce wanda ake zargin ya ce ya kashe ‘yar ne saboda ta ga ya aikata laifin kashe mahaifiyar. Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin a jiya kuma ya amsa laifinsa.
Kiyawa ya ce ‘yan sanda sun fara bincike kan laifin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇