Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama wani matashi, mai suna Abba Garba wanda akafi sani da (Dan Kuda) bisa zarginsa da hallaka Zaharaddin Iliyasu, ta hanyar yankan rago sakamakon sun samu sabani da marigayin.
Alfijir labarai ta rawaito Kakaki rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manaima labarai da yammacin ranar Asabar.
Rahotanni na cewa lamarin ya faru ne a yankin Sabontitin Phanshekara karamar hukumar Kumbotso dake jahar, tun a daren ranar Juma’a 29-3-2024.
SP Kiyawa, ya ce jami’an yan sandan Panshekare ne suka samu nasarar cafke matashin, a lokacin da yake kokarin guduwa jamhuriyar Nijar .
Yanzu haka dai ya na tsare a hannun yan sandan domin ci gaba da amsa tambayoyi kafin a gurfanar dashi a gaban kotu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk