Birtaniya Ta Hana Matafiya Daga Najeriya Shiga Kasarta
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Kasar Birtaniya ta haramta wa matafiya daga Najeriya shiga kasarta saboda bullar kwayar cutar COVID-19 samfurin Omicron.
Jaridar Aminiya ta rawaito Hukumomin kasar sun sanya sunan Najeriya a cikin jerin kasashen da ta hana bakinsu shiga kasarta ne a ranar Asabar.
Best Seller Channel
Wata sanarwar da Gwamnatin Birtaniya ta fitar ta ce, “Za a sanya Najeriya a cikin jerin kasashen daga karfe 4 na asuba ranar Litinin 6 ga Disamba saboda bullar kwayar cutar Omciron da aka samu a kasar da kuma mutum 134 da suka harbu da ita a fadin kasar Birtaniya.
A makon nan ne da dai Hukumar Yaki da Cututttuka Masu Yaduwa (NCDC) ta tabbatar da harbuwar mutum uku da kwayar cutar Omicron a Najeriya.
Umarnin bai shafi matafiya ’yan kasar Birtaniya da mazauna da ’yan kasar Irelanda ne kadai za a bari su shigo kasar daga Najeriya.
Best Seller Channel
Su ma din, “Wajibi ne a killace su na tsawon kwana 10 a cibiyoyin da gwamnati ta tanadar inda za a yi musu gwajin PCR sau biyu, a matsayi matakin dakile kwayar cutar.”
Sai dai ta ce matakin da ta dauka na wucin gadi ne a halin yanzu
Best Seller Channel