Bamu Da Ikon Sauke Farashin Gas- Gwamnatin Tarayya

 

Ba za mu iya sauke farashin gas ba a halin Yanzu! 

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana wasu dalilai da suka hana ta taɓuka komai a game da hauhawar farashin gas a ƙasar nan.
 Jaridar Manhaja ta rawaito Gwamnatin ta bayyana cewa, abin ya fi ƙarfinta ne, saboda ita iskar gas gwamnati ba ta ɗauke mata tallafi ba, sannan kuma farashinta ikon kasuwannin ƙasashe ne ba ƙasa guda ba.
Timipre Sylva shine Ministan albarkatun man fetur, ya bayyana haka a ranar Talatar da ta wuce a yayin da yake mayar da martani a game da tambayar da aka yi masa kan dalilin da ya kawo tashin gwauron zabi na farashin gas ɗin girki abinda ya tilasta wasu ‘yan ƙasa amfani da wasu makamashin saɓanin gas ɗin. 
Best Seller Channel 
Ministan ya ce, “Gwamnatin Tarayya ba za ta iya komai ba don shawo kan matsalar tashin farashin na gas ɗin ba”
idan za a iya tunawa, farashin na gas kwana-kwanan nan ya yi matuƙar tashi a Nijeriya, inda har ya ninka fiye da kuɗin da ake sayar da shi a baya. 
Abinda ya jawo wasu magidantan suka fara komawa amfani da icce ko gawayi domin an cire tallafin kan gas ɗin.
 Sannan kuma harajin VAT na shigo da gas din daga ƙasashen waje shi ma ya taimaka wajen hauhawar farashinsa. 
Gwamnati ba ta da iko a kan hawa ko saukar farashin gas ɗin, abu ne da ya shafi dukka ƙasashen Duniya.
Best Seller Channel 
Ministan ya ƙara cewa, a yanzu haka a ƙasar Turai ma an samu irin wannan makamanciyar hauhawar farashin na gas abinda ya jawo aka yi zanga-zangar rashin amincewa.
 To yanzu zancen da ake yi, farashin gas ɗin nahiyar Turai shi ya jawo hauhawar farashin gas a faɗin Duniya. Wannan da ma kuma ƙarin harajin VAT a kan gas dukka sun taimaka wajen ƙaranci da tsadar gas ɗin. 
Hakazalika, yawan shigo da gas ɗin daga ƙasar waje shi ne ya kashe kasuwancin samar da gas na cikin gida, a Nijeriya. 
A cewar Ministan waɗannan dalilai su suka sa gwamnati ta kasa saita farashin gas ɗin yadda za ta sakko da shi. 
Amma Shugaba Muhammadu Buhari yace suna nan suna iya ƙoƙarinta wajen ganin sun kawo ƙarshen tashin farashin nasa. Domin sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya tsadar rayuwa
Best Seller Channel 

Slide Up
x