Budaddiyar Wasika Daga Tsohon shugaban Ma’aikatan Jihar Kano Alh Usman Bala

IMG 20231028 WA0006

Alhamdu Lillah! Alhamdu Lillah!! Alhamdu Lillah!!!

Ni Alh Usman Bala Muhammad Mni., ina mai matukar baiyana godiya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala; da yabani ikon hidimtawa jihata (Kano), a matakai daban daban har na zamo shugaban ma’aikata na jihar Kano baki daya.

Ina kara gode masa (Subhanahu wa Ta’ala) da yasa na kamala wannan aiki lafiya, ta hanyar ajiyewa domin radin kaina, musamman domin bayarda dama ga wasu, suma suzo su bada gudunmawarsu wajen ciyar da jiharmu (Kano) gaba.

Ina rokon Allah tabaraka wa Ta’ala ya sanya albarka a cikin dukkanin gudun mawar da nabayar, musamman a matsayina na shugaban ma’aikatan jihar Kano, wajen inganta harkar aiki da kuma walwalar ma’aikata (masuci da wadanda sukabar aiki).

Ina kara rokon Allah, ya cika mana ladan abubuwan da makayi daidai, ya kuma yafe mana inda mukayi kuskure.

Har ila yau, ina godewa mai girma gwamnan jihar LKano Engr. Abba Kabir Yusuf, musamman saboda hadinkan daya bani ta hanyar sauraro, tuntuba, da kuma karbar shawarwari.

Bugu da kari, ina kara godewa mai girma gwamna bisa amincewa da yayi da bukatar da namika masa ta ajiye aikina a daidai wannan lokaci.

Bugu da kari, ina godiya ga dukkannin gwamnonin jihar Kano wadanda nayi aiki tare dasu a matakai daban daban (Dr. Mal Ibrahim Shekarau, Engr. Dr Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Dr. Abdullahi Umar Ganduje) bisa karamcinsu na nadani mukamai daban daban, amincewa, da kuma hadinkai domin gudanar da aiyukan da suka kamata.

Ina godiya ta musamman ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda a lokacin gwamnatinsa ne na fara zama shugaban ma’aikatan jihar Kano baki daya, a lokaci guda kuma ya bani shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar kano.

Suma ma’aikatan jihar Kano, bazan taba mantawa dasu ba wajen mika godiya mai tarin yawa, saboda cikakken hadin kai da goyon baya da suka bani wajen jagorancinsu, har muka sami irin dimbin nasarorin da muka samu.

Ina rokon Alla ya saka musu da Alheri yasa suma su gama aiki lafiya.

kuma ina fata duk wanda Allah zai kawo a matsayin sabon shugaban ma’aikata to a bashi hadinkai da goyon baya kamar yadda aka bani.

Haka kuma, ina godiya mai tarin yawa ga yan’uwana na jini, iyalina, da kuma abokan arzika daban daban saboda dinbin gudumawarsu a gareni da kuma hakuri da yadda bukatun aiki suke taba walwalar mu’amala a wasu lokuta.

Daga karshe ina rokon Allah ya gafartawa mahaifana, Allah ya kyautata makwancinsu, domin sune suka bani ginshikin kyakkyawar tarbiyar wadda taimini linzamin zama da jama’a lafiya tare da girmama na gaba da kuma adalci ga na kasa.

Nagode Naku
Usman Bala Muhammad Mni.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *