Budaddiyar Wasika Ga Gwamnan Kano Akan Wata Ƙatuwar Matsala A Asibitin Nassarawa

Kano ce

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu da fatan kana lafiya Allah ya inganta lafiya Ameen.

Mai girma gwamna na gano wani babban al’amari a cikin asibitin Nasarawa mara daɗi! Duk kokarin da kake yi a fanni lafiya amma wannan lamarin ya zama sai hamdak

Ranka ya dade binciken da muka gudanar a bangaren masu haihuwa na asibitin Nasarawa mun gano cewar, duk girman asibitin nan da darajarsa da kuma kwararrun ma’aikatan da yake da shi a ciki ace wai sahin karɓar haihu gado guda tara 9, ne gare shi a ciki! Bangaren wadanda suke da barazanar kamuwa da larurar jijjiga kuwa gado guda huɗu 4, ne kacal, kuma duk yawan bayin Allah da suke zuwa wannan sashin a kullum ace masu kula da su su biyu ne kawai a shirtin, masu shara da goge-goge mutum daya!

Mai girma gwamna na leka wani makeken daki dake wajen a rufe, sai na tambaya inane nan, sai aka cemin ai tiyatace aka gina amma ba a zuba kaya a cikinta ba! Babban abin takaicin ga mutane an rasa inda za a saka su saboda rashin waje, sannan ga daki an rufe ba komai a cikinsa! To me yasa idan ma ba za a gina sabon wajen da zai dau jama a da yawa ba to a zubawa wannan dakin gadaje mana.

Mai girma gwamna kai da kanka ka sanar da samarwa da masu haihuwa kayan haihuwa kyauta a jihar nan, amma shima fa abin yana neman zama rijiya ta bada ruwa guga zai hana.

Don haka nake kira gareka, idan kayan haihuwa kyautar nan da aka shelanta ba su isa ga asibitocinba ko kuma sun yi ƙaranci ne to a dau mataki akai.

Mai girma gwamna ina kara kira a gareka akan abinda idona ya gani a asibitin Nasarawa bangaren haihuwa lamari ne mara daɗi da zai iya kawowa gwamnatinka nakasu da kuma jihar baki ɗaya.

A karshe nake maka addu’ar Allah yayi riko da hannunka kan ayyukan alheri da ake bijiro da shi a jihar nan musamman harkar lafiya da ilimi.

Mai biyayya a gareka
Musa Ahmad Durumin iya
Best Seller

Editan Alfijir labarai/Alfijir News

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *