Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, a kunshin tsohon gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wato Alhaji Muhammad Sanusi Kiru, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka gudanar da aikin mayar da makarantar Government Girls Secondary School (GGSS) Maikwatashi zuwa Kaura Goje, inda ya ce an yi manyan kura-kurai.
A cikin wata wasika da ya rubuta ga Gwamnan Kano, Kiru ya ce, duk da cewa ya yaba da kokarin gwamnatin jihar wajen inganta harkar ilimi, amma yadda aka gudanar da wannan aikin ba dai-dai ba ne.
Ya tuna cewa a lokacin da aka yi irin wannan sauyi a zamanin yana kwamishina, a makarantar Jido Primary School, sai da aka gina sabuwar makarantar gaba ɗaya, aka samar da kayan aiki da kujeru, kafin a mayar da ɗalibai, Wanda hakan ya taimaka wajen kauce wa matsaloli da tsaiko ga karatun yaran.
A cewar Kiru, “Abin takaici, ba a yi Irin wannan tsarin akan makarantar Maikwatashi ba. An rusa tsohuwar makaranta kafin a kammala sabuwar, abin da ya janyo wa ɗalibai, malamai da al’umma wahala da rudani, lamarin da ya nuna cewa masu kula da aikin sun nuna rashin kwarewa da sanin Makaman aiki wajen tafiyar da irin wannan tsarin mai sarkakiya”.
Haka kuma, tsohon kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan hujjojin da aka bayar wajen tashin Makarantar ta Maikwatashi, musamman yadda aka nuna al’ummar Sabon Gari a matsayin masu laifi da ’yan daba, adan haka ya ce wannan kalami bai dace ba, musamman la’akari da irin gudunmawar da wannan al’umma su ke bayarwa ga ci gaban jihar, da kuma yadda su ka taka rawa wajen zuwan Wannan gwamnatin a zaben shekarar 2023.
Kiru ya kuma bayyana damuwarsa kan labarin cewa filin tsohuwar makarantar ana siyar da kowanne fuloti akan naira miliyan ɗari (₦100,000,000), wanda ya ce a maimakon haka kamata ya yi gwamnatin ta mayar da wurin filin wasanni, dakin taro ko wani abu da al’umma za su amfana.
Ya kuma soki maganganun da mai baiwa gwamnan kano shawara na musamman kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yi a cikin wani faifan bidiyo, yana cewa bai kamata wanda ba shi da ruwa da tsaki a harkar ilimi ya rika magana kan irin wannan batu ba.
Daga bisani tsohon Kwamishinan ya yabawa kwamishinan ilimi na yanzu bisa yadda ya guji tsoma ma’aikatarsa cikin rikicin, yana mai cewa har yanzu akwai damar gyara kura-kuran da aka tafka.
A karshe, Kiru ya bukaci gwamnati ta dauki darasi daga wannan al’amari, domin ta inganta tsarin kula da harkokin ilimi a jihar cikin gaskiya, tsari, da tuntubar masu ruwa da tsaki.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t