Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusif Daga Hamisu Iyantama

FB IMG 1718022234949

Shawara zuwa ga Mai girma Zababben Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusif.Gida-Gida.

Da farko Ina ta yaka murnar cika Shekara Daya akaragar Mulki.

Muna godiya da irin kamun ludayin jagorancin da ka keyi a wannan Jiha ta Kano.

Shawara ta 1.kamar yadda Gwamna ka kaddamar da State of Emergency akan harkar ilmi ranar asabar a farfajijar gidan Gwamnatin Kano tare da diban sabbin Malamai na Besda. Al,ummar Kano sun yaba maka, kuma suna godiya.

A sakamakon haka nake bada shawarar Gwamna kayi kokari wajen saka State of Emergency akan harkar Hauhawar farashin kayan masarufi da Kwacen Waya…domin Hauhawar farashin ba gaira ba dalili ya ragargaza Tattalin arzikin Jihar Kano.

Mai girma Gwamna Wallahi Al,ummar Kano da kananan ‘Yan kasuwa suna cikin wani Hali na matsi da rugujewar jari, suna cikin halin wayyo Allah,Al,amarin ya  ya wuce misali fiye da yadda kake samun Labari.

Kullum Muna shiga cikin Kasuwanni muna zama a majalisu da mutane muna jin koken su.. Gwamna al,ummar Kano na cikin wani yanayi Wallahi rubutu na bazai iya fayyace maka irin radadin da Kanawa da sauran al,ummar arewacin kasar nan ke ciki ba.
Ina kara bada Shawara cewa atakawa ‘Yan kasuwa birki cikin gaggawa ayi doka akan Karin farashin ko akafa wata hukuma da zata dinga kula da wannan al,amari akowacce Karamar hukuma.

Kamar yadda mai girma Gwamna akwana 2 kacal akayi wata doka kwanan nan a kano, toh Ina bada Shawara da Majalisar Kano acikin kwana biyu suyi dokar ta baci dangane da hauhawar farashin kayan masarufi da Kwacen waya.wadannan Al,,amura na ciwa kafatanin al,ummar Kanawa da makwabtan su tuwo akwarya fiye da tunanin masu tunani…ko Kuma kuyi hadin gwiwa da sauran Gwamnonin Arewa da kasa baki daya domin shawo Kan wannan matsala.

Mai girma Gwamna na fahimci irin kokarin da kake Yi afannoni lafiya,naga ka mayar da hankalin ka sosai ,muna godiya amma akwai bukatar yadda kake yawan ziyartar Asibitin Hasiya Bayero domin inganta shi da ganin komai na tfy yadda ya kamata toh ka dinga ziyartar sauran asibitocin Mussanman Manyan asibitocin Kano, Wallahi akwai matsaloli masu dunbun yawa amma nafi so kayi ziyarar bazata akai -akai wataran zaka fahimci irin sakon da nake so in nusar maka.

Akwai shawarwari masu dinbun yawa a tattare dani,nayi iya kokarin ganin ka domin bada su Kai tsaye amma ganin ka yayi wuya, ya gagare ni..Wannan  yasa nace bari inyi budaddiyar wasika a matsayina na Wanda yayi  kokarin ganin ka samu nasarar hawa wannann kujera ta Gwamna domin inada yakini da nake dashi cewa Kai adali ne kuma mai sauraren Jama,ar ka ne birni da kauye..

A kullum ‘Yan uwan mu ‘Yan adawa idan mun hadu muna samun shagube da kananan maganganu cewa Gwamnatin mu ta gaza,ni Kuma nasan baka gaza ba kana iya kokarin ka, amma Jama,a basa gani..Ina addu,ar Allah ya ganar dasu Amin..

Sai Kuma maganar Yan Jam,iyar NNPP/Kwankwasiyya da suka bada gagarumar Gudunmawa wajen zaben ka da sauran kujerun Senatoci da ‘Yan majalisu anan bagaren ma ana korafi mai yawan gaske, da yawa a yanzu sun shiga halin ha’u la’i akwai sunayen wasu cikin kwamitocin kanfen dinka sunyi kokari sosai, sun bada lafiyar su da dukiyar su, da lokacin su, wasu kuma da Kwakwalwar su a lokacin kanfen, amma yanzu suna kwamflen sosai wasu suna fitowa radio suna nuna bacin ran su cewa ganin ka ya gagare su koda kuwa da gaisuwa, ku gaisa ku dauki  hoto don su nuna Kuna tare, amma hakan su yaki cimma ruwa. wasu kuma sunyi zaton tun a dibar fari za,a tafi dasu amma zunji Shiru, duk inda na tsaya sai korafe korafe kala-kala.

Mai girma Gwamna ka kafa wani Kwamiti da zai za kulo maka irin wadannan mutane da Suka so ka so na Hakika, domin fara zaman tattaunawa dasu…domin suna shan gorin cewa an tura mota…

Mai girma Gwamna mu gani akasa ka karyata abokan adawa, ka nuna kana sane da mutanen ka, ataimaki wadanda suka taimaka domin ni buri na, Allah ya baka Ikon yin tenure Biyu har ka kafa wani Gwamna da zai dora akan ayyukan ka.

Allah yasa wannan sakon yazo gare ka cikin fahimta da gane me nake nufi..

Anan zan tsaya chak sai Kuma wani jikon domin maganganu dake baki na da yawa..

Nine dai Wannan Masoyin wannan Gwamnati ta NNPP Kuma Mai kaunar Gwamna da ci gaban Gwamnatin sa.

Alh.Hamisu Lamido Iyantama
Kano Nigeria.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *