Yan Jarida Sun Kauracewa Dukkanin Wasu Harkoki Na Gwamnatin Jihar Kano Ba Tare Da Bata Lokaci Ba

Screenshot 20240610 152052 Chrome

Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta kasa, ta ce ta kauracewa dukkanin wasu harkoki na gwamnatin Jihar Kano ba Tare da Wani bata Lokaci ba.

Alfijir labarai ta ruwaito matakin hakan na kunshe cikin Wata sanarwar da shugaban kungiyar Aminu Ahmed Getso ya sanyawa hannu a litinin din nan.

Getso ya bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne saboda kyara, da cin Fuska da tsangwama da ya ce wakilan nasu na fuskanta daga gwamnati da wakilanta yayin gudanar da aiyukansu

Kazalika kungiyar ta koka kan yadda ta ce, gwamnatin na amfani da wadanda ba yan yaridu ba wajen daukar harkokin gwamnati, maimakon barin yar jaridu su yi aikinsa bisa kwarewa.

Saboda haka ne kungiyar ta ce daga yanzu ba zata sake halartar taron yan jaridu, ko wata ganawa da wakilan gwamnati ba, har sai an samu gyara kan ‘yanci da kuma kare lafiyar yan jaridu a fadin jihar.

Ana Samun Korafe Korafe akan Yadda Gwamnatin Jihar Kano take Watsi da ka’idar aikin Jarida Wajen baiwa Yan Siyasa Damar Wasu ayyuka Wanda Kuma hakan ya Saba da Dokar aikin Jarida

Ko a Hawan Karamar Sallah da ya gabata sai da aka samu wata Hatsaniya a Gidan Gwamnatin Jihar Kano Tsakanin Wani Jami’in Gwamnati da Kuma wasu Yan jaridu sakamakon Kokarin shiga Aikin Yan Jarida da akeyi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Slide Up
x

One Reply to “Yan Jarida Sun Kauracewa Dukkanin Wasu Harkoki Na Gwamnatin Jihar Kano Ba Tare Da Bata Lokaci Ba”

  1. I’m very proud of the way you present the news, & highly concern at the same time appreciate your action towards the report of what took place between the Kano state government and the journalist.
    Charity begin’s at home.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *