Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu ya mai girma gwamna, sakon al’ummar karamar hukumar Kumbotso ne suka aiko wa Alfijir labarai domin isa gareka.
Sakon ya fara da cewa
Kwamitin iyaye da ‘yan uwa, da magoya bayan ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso a jami’ar NNPP, Hon Ali Musa Danmaliki (Hard Worker), ya gudanar da taron manema labarai a yau Litinin 28, Oktoba 2024, don sanar da al’umma da gwamnatin jihar Kano, matsaryasu akan nasarar da ya samu a zaɓen kananan hukumomin jahar Kano, wanda ya wakana a ranar 26 ga watan Oktoba, 2024.
Taron ya mayar da hankali ne wajen kira ga Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya bi umarnin babbar kotun jihar Kano mai lamba 4, wajen rantsar da Hon Ali Musa Danmaliki, a matsayin halattaccen shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso bisa nasarar da ya samu a zaben ranar 26 ga watan Oktoba, 2024.
Mataimakin Darakta Janaral na kwamitin yakin neman zaben Hon Ali Musa Danmaliki (Hard Worker) 2024 Hon Jabiru Abdullahi Zawachiki, ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano, da ta mutunta umarnin babbar kotun jahar Kano, wajen rantsar da Hon Ali Musa Danmaliki, a matsayin shugaban hukumar Kumbotso.
Ya ƙara ƙasa da cewar “Hon Ali Musa Danmaliki (Hard Worker) shi ne halattaccen Dan takarar, kuma shi ne ya shiga zaben da ya gudana a ranar 26 ga watan Oktoba na wannan shekarar. Mu bamu da ikon janye kara ko yin yafiya akan hukuncin da kotu ta yi, domin yanzu magana ce ta hukuncin kotu wanda ya riga ya zama doka.
Hakazalika wannan matsayar tamu bata da wata alaka ta kusa ko ta nesa da wani jagora a karamar hukumar Kumbotso, wannan matsaya ce ta kashin kanmu mu magoya bayan.”
” Mun yarda da cewa addu’a da jajircewa sune suka kawo mu ga wannan mataki na nasara da muka hau, kuma lallai addu’a ce za ta ci gaba da yi mana jagoranci akan duk wani abu na nasara da za su taso a nan gaba,”
“Muna kira ga mai girma Gwamnan jihar Kano, bisa yadda doka ce ta kawo shi kuma doka ce ta tabbatar da a zabi shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, a matsayin dan takara halattacce a cikin tutar jam’iyyar NNPP a jihar Kano.
Kuma Alhamdulillahi wannan babbar kotun jihar Kano, ta yi hukuncin tabbatar da Hon Ali Musa Danmaliki a matsayin halattaccen dan takara wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takara a wannan zabe da ya gudana, kuma muna kira ga mai girma Gwamna da ya taimaka ya sa a rantsar da Hon Ali Musa, kamar yadda aka rantsar da sauran shugabannin kananan hukumomi 43 a jihar Kano, shi kadai ne ya rage ba a rantsar ba, to muna kira ga mai girma Gwamnan jihar Kano da yi wannan abu, domin tabbatar da adalci da daidaito a cikin wannan karamar hukuma.”
“A karshe muna yi wa mai girma Gwamna fatan alheri Allah ya taimaki gwamnatinsa kuma ya yi masa jagoranci abisa abin da yake son aiwatarwa na alheri, muna fatan Allah ya zaunar da jihar Kano lafiya da Kumbotso lafiya.
Adamu Garba Bechi daya ne daga cikin daraktocin yakin neman zaben Hon Ali Musa Danmaliki (Hard Worker), ya ce maganar Hon Ali Musa Danmaliki, magana ce ta al’ummar ƙaramar hukumar Kumbotso baki daya. Inda ya ce,
“Muna kira da babbar murya da a gaggauta rantsar da Hon Ali Musa Danmaliki, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a karamar hukumar Kumbotso.
Karamar hukumar Kumbotso ƙaramar hukuma ce mai mahimmancin gaske a jihar Kano, taɓa zaman lafiyar ta, zai iya shafar zaman lafiyar jihar Kano, kuma mun san Gwamna mai bin doka da oda ne, kuma muna tabbatar masa kin bin wannan umarni abu ne da ba zai haifar da ɗa mai ido ba, wannan sako ne na ƙaramar hukumar Kumbotso, ba wai sakon ne na Hon Ali Musa Danmaliki ba. Doka ce tai gwamnati kuma doka ce ta kawo shi, mun bi duk ƙa’idar da yakamata mu bi, to muna tabbatar da a bi wannan ƙa’ida cikin gaggawa domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a karamar hukumar Kumbotso, dama jihar Kano, baki daya.”
Al-Manasik Reporters, ta rawaito cewa, a ranar 25 ga watan Oktoba, 2024, babbar kotun jihar Kano mai lamba 4 karkashin jagorancin Mai Shari’a Usman Mallam Na’abba, ta tabbatar da Hon Ali Musa Danmaliki, a matsayin halattaccen dan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso a jam’iyar NNPP, biyo bayan shigar ƙarar da Hon Ali Musa Danmaliki ya yi a gaban kotun, inda yake kalubalantar shugabancin jam’iyar na jihar Kano, bayan canja sunansa da ta yi da sunan Abdullahi Ghali Shitu, a matsayin wanda zai yi wa jam’iyar NNPP takara a karamar hukumar Kumbotso, ba Hon Ali Musa Danmaliki ba.


Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj