Buhari ya nada Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero Chancellor


Best Seller Channel 

Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban jami’ar Calabar ta jihar Cross River. 

 Shugaban Jami’ar, Janar Matthew Luther Agwai (RTD) ne ya bayyana hakan, a ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da ya jagoranci mambobin majalisar a ziyarar taya murna da suka kai wa Sarkin a fadarsa. 

Shugaban ya ce al’ummar Jami’ar Calabar ta cika da murna da nadin da aka yi wa Sarki Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Shugaban Jami’ar. 

Ya ci gaba da cewa da gogewar sarkin, zai jami’ar za ta samu babban matsayi na ƙwararrun ilimi. 

Best Seller Channel 

Muna tattaunawa da jami’ar Calabar da ke Jihar Kuros Riba, kuma za mu yi iya kokarinmu wajen ganin an samu Nagartaccen Ilimi 

“Mai Martaba Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero  ya nemi goyon bayan daukacin ‘yan Majalisar da Jami’ar wajen ganin cewa an cika burin da ake so.

 Daga nan sai ya yaba da namijin kokarin da Shugaban Jami’ar, Janar Matthew Luther Agwai, da ‘yan uwa na Jami’ar suka yi, inda ya bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin.