Cigaba! Matatar Man Dangote Ta Fara Sarrafa Man Fetur A Najeriya

Matatar Dangote

Matatar man Dangote, ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan.

Alfijir Labarai ta rawaito wani jami’in gudanarwar matatar ne ya bayyana haka a ranar Litinin.

Matatar da darajarta ta kai dala biliyan 20, ta fara aiki ne a watan Janairu tare da samar da kayayyakin da suka hada da man jiragen sama.

Ita dai matatar zata dinga fitar da gangar mai 650,000 a kowace rana, kuma mafi girma a Afirka, an yi alkawarin za ta saukaka tsadar mai da kuma dogaro da man da ake shigowa da shi daga kasashen waje.

“Muna gwada samfurin (man fetur) kuma daga baya zai fara kwarara cikin tankunan da ake samarwa,” in ji Devakumar Edwin, mataimakin shugaban kamfanin Dangote.

Sai dai bai bayyana takamaiman lokacin da man fetur din zai fara shiga kasuwanni ba.
Edwin, ya ce kamfanin mai na kasa (NNPC), kadai za su sayar wa man fetur.

“Idan har kuma babu wanda ke saya, za mu fitar da shi zuwa kasashen waje kamar yadda muke fitar da man jirage da dizal,” in ji shi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *