Cigaba: Najeriya ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man fetur uku.

IMG 20250308 150707

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku.

Alfijir labarai ta ruwaito cikin wata sanarwa hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun ne a jihohin Abia da Delta da kuma jihar Edo.

NMDPRA ta ce sabbin matatun uku idan an kammala su za su iya tace gangan 140,000 a kowace rana.

Bayanai daga hukumar ta NMDPRA sun nuna cewa Najeriya na da matatun man fetur tara, ciki har da sabuwar matatar Dangote da ke birnin Legas.

Waɗannan matatu na tace ganga 974,500 a kowace rana, yayin da matatar Dangote kaɗai ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *