Cikakken rahoton kama Murja Kunya da EFCC tayi a kano

FB IMG 1742210892864

Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon-kasa EFCC reshen jihar Kano sun kama shahararriyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya bisa zargin cin zarafi da lalata Naira.

An kama Murja Kunya ne da laifin liƙa takardar kudin Naira domin jin dadi a lokacin da take zama a dakin otal da ke Tahir Guest Palace a Kano. Kamen dai ya biyo bayan zawarcin da jami’an EFCC suka yi mata ne bayan da ta tsallake belin da hukumar ta yi mata tsawon wata daya da ya wuce.

Tun da farko an kama ta ne a watan Janairun 2025 da laifin karya dokan babban bankin Najeriya CBN, da ta haramta cin zarafi da lalata Naira. Hukumar ta bayar da belin ta inda aka gurfanar da ita a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano. Duk da haka, lokacin gabatar da ita a kotu ya yi, Kunya ta gudu, ta kauce wa tsarin shari’a.

Sai dai kuma bayan kwashe tsawon makonni ana bincike da kuma sa ido, jami’an EFCC sun yi nasarar sake cafke jarumar na TikTok a ranar Lahadi 16 ga Maris, 2025. Daga nan kuma aka mika ta zuwa Hukumar Shiyya ta Kano, inda a halin yanzu take tsare tana jiran a gurfanar da ita a gaban kuliya.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *