Cin Hanci Da Rashawa Ya Bunƙasa Ne Ta Yadda ’Yan Siyasa Ke Baiwa Jama’a Wani Kaso Na Dukiyar Da Suka Sace – In Ji Sanata Ndume

FB IMG 1715518896576

Sanata Ali Ndume, babban mai Tsawatarwa a majalisar dattawa, yayi tsokaci kan batun cin hanci da rashawa.

Alfijir labarai ta ruwaito Ndume ya jaddada cewa cin hanci da rashawa a siyasar Najeriya na da nasaba da wasu mutane, wanda Hakan na Iya haifar da koma baya a kasar.

Yayin da yake amincewa da wanzuwar cin hanci da rashawa a tsakanin ‘yan siyasa, Ndume ya kuma yi nuni da cewa, galibi suna rarraba kuɗaɗen ne ga jama’a.

Yace, “Idan aka kwatanta girman cin hanci da rashawa a tsakanin ‘yan siyasa, ya yi kadan. Al’umma ce ke tafiyar da almundahanar mu. ’Yan siyasa sukan yi ta raba kuɗaɗen da suka samu Ga jama’a ba bisa ka’ida ba. Idan ba su yi ba, suna haɗarin rasa goyon baya kuma ba za a sake zaɓe su ba.

“Ina da gogewa a Majalisar Dokoki ta kasa, duk da yake ina goyon bayan hukunci mai tsauri kan cin hanci da rashawa, kamar hukuncin kisa, bai kamata a aiwatar da shi ba gaira ba dalili, misali, wanda ya saci kadan bai kamata ya fuskanci hukunci daidai da wanda ya wawure biliyoyin kudade daga Gwamnati ba.

“Hukuncin kisa na iya zama abin hana aikata laifukan da suka shafi muggan kwayoyi, Saboda yana nuna girman laifin. Fataucin muggan kwayoyi ba wai yana lalata rayuka ba har ma yana haifar da asarar rayuka,” in ji Ndume.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *