CP Dogo Ya Magantu Kan Alaƙar Ƴan’uwantaka Tsakaninsa Da Sarki Aminu Ado Bayero

FB IMG 1719573758629

Sabon Kwamishinan Ƴan sandan  jihar Kano, Salman Garba ya musanta zargin cewa shi ɗan uwa ne na jini ga Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

  Alfijir labarai ta ruwaito Kwamishinan ya ce bashi da alaka da Sarki Bayero kuma shi ya zo Kano ne don yi wa ƙasa aiki, ya bayyana haka ne a taron manema labarai a ofishin sa

A cewar sa, zai yi aiki ne yadda doka ta tanada ba tare da nuna bambanci addini da yare ba.

Ya ce zai samar da wani tsari mai ƙarfi wajen samar da zaman lafiya tare da bin doka da oda, in da ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne babbar manufar sa.

Ya kuma ci alwashin yakar dabanci da ya addabi jihar a kwananan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *