Kwamitin Majalisar wakilai mai yaki da cutar zazzabin cizon sauro, HIV/AIDS, da tarin fuka, Ya gayyaci Mohammed Pate, ministan lafiya da walwalar jamaāa, kan zargin karkatar da dala miliyan 300 na kuÉaÉen yaki da zazzabin cizon sauro.
Alfijir labarai ta rawaito shugaban kwamitin,Amobi Ogah ne ya sanar da hakan a wani zama da suka yi a Abuja A Yau Talata.
Ogah ya nuna rashin jin dadinsa da rashin halartar babban sakatariyar maāaikatar a taron kwamitin, inda yace idan har ta gaza bayyana bayan sammaci uku, za a kama ta.
“Maleriya ta zama annoba a Najeriya, duk da cewa Gwamnati ta ware kudade tun daga Shekarar 2021. Sai dai a mafi yawan lokuta ma’aikatan Gwamnati na haifar da kalubale,” inji Amobi Ogah.
Ya jaddada cewa wannan ita ce gayyata ta uku da aka yi wa sakatare na dindindin domin fayyace yadda ake amfani da kudaden. Kwamitin na neman amsoshi kan ko an yi amfani da kuÉaÉen da kuma inda suke a halin yanzu.
āShin sun yi amfani da kudin? Idan ba su yi amfani da kuÉin ba, ina kuÉin? Magana ce mai sauĘi. Amma sun yi ta gudu suna kiran mutane iri-iri domin su yi magana da mu,ā inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai š
Majalisa https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk