Da Ɗumi Ɗuminsa! Hukumar Yan Sandan Jihar Kano Ta Karrama Asma u Baby Nayis

Alfijr

Alfijr ta rawaito kwamishinan yan sandan jihar Kano Cp Sama’ila Dikko ya Karrama wasu fitattun yan jarida a yayin Walimar da aka shirya masa ta kammala aikinsa a jihar Kano

Asma u Sadiq wacce ake wa lakabi da Baby Nayis, ma aikaciyar Dala Fm a Kano ta sami wannan Karramawar, duba da irin yadda take bawa rundunar gudunmawar wajen wayar da kan al umma a Jihar nan.

Alfijr

Baby Nayis a tattaunawar ta da Alfijr yayin taron, ta godewa Allah bisa wannan karramawar da aka zakulota cikin zaratan yan jarida a cikin wannan jiha.

Sannan ta kara kira ga yan uwa yan jarida da su dage wajen yin aikinsu tsakaninsu da Allah, sakamako na nan tafe.

Asma’u Baby Nayis itace program Manaja ta Dala, kuma itace mawakiyar gada ta farko a jihar Kano, sannan kuma itace mai gabatar da shirin Kaddara ko ganganci Wannan rayuwa, Tafa tafa, da sauran shirye a Dala Fm da Freedom Radio

Alfijr
Muna daga alfijr Labarai muna taya Baby Nayis da sauran wadanda suka sami wannan Karramawar murya, Allah ya sanya alkhairi ameen.

Slide Up
x