Gwamnatin Taraiyya Ta Dakatar Da Kanfanin Jiragen Sama Na Dana Air

Alfijr

Alfijr ta rawaito Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa, NCAA ta sanar da dakatar da lasisin zirga-zirgar jiragen sama na Dana Airlines (ATL)

Sannan kuma ta bada takardar shaidar yin amfani da jiragen sama (AOC) har sai baba-ta-gani.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daracta janar na hukumar Musa Nuhu, ya sanyawa hannu a jiya Laraba a Lagos. wanda ya nuna cewa Dana Airlines ya gaza cika wajibcin kudi da gudanar da ayyukan jirgin lafiya.”

Alfijr

An dakatar da lasisin aiki na Dana bayan da hukumar “ta gano cewa kamfanin jirgin ya gaza cika wajibcin biyan kuɗaɗe da kuma gudanar da tashi da saukar jiragensa lafiya kamar yadda doka ta tanadar.

Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa, an dakatar da shi ne bisa ga sashe na 35 (2), 3 (b), da (4) na dokar zirga-zirgar jiragen sama, 2006 da kuma sashi na 1.3.3.3 (a) (1) na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya.

Slide Up
x