Da Ɗumi Ɗuminsa! Gwamnati zata cire Masarautu daga Karkashin kulawar Kananan Hukumomi

Mai Baiwa Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago Shawara na Musamman akan harkokin bunkasa Masarautu Hon. Abdulmalik Cheche Shine ya bada tabbacin haka, A zantawar sa da Jaridar Tsalle Daya.

Cheche yace shirye-shirye yayi nisa na wani tsarin da za’a fitar a Jihar Neja, wanda zai tsame Masarautu daga dogaro da Kananan Hukumomi.

A cewar sa shirin zai mayar da hankali wurin inganta Albashin Dakkatai da Hakimai tare da Gina musu gidaje da kuma siya masu ababen hawa.

Ya kuma ce Gwamnan ya sauya Salo na dakatar da sarakuna zuwa fadar Gwamnati.

Maimakon haka duk lokacin da suke da bukatar sa shi zai je har fada domin basu darajar da Allah ya basu.

Ya koka da yadda cewa ko turawan mulkin mallaka basu raina sarakuna ba, Amma a yanzun wasu na amfani da damar da suka samu suna raina ubannin kasa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *